Ni na sa City take yin nasara - Mancini

Roberto Mancini
Image caption Kocin ya bugi kirjin shi ya kawo 'yan wasa dake zura kwallaye a City

Tsohon kocin Manchester City Roberto Mancini ya ce ya taka gagarumar rawa wajen samun nasara da City ta keyi a wasanni a kakar bana.

Ana ta yabawa sabon koci Manuel Pellegrini a kan yadda ya gyara kungiyar da tuni ta zura kwallaye 106 a bana da sawa kungiya matsi idan suna karawa wasa.

Sai dai kocin Galatasaray wanda yabar kungiyar a bara, ya ce 'yan wasan da ya sayo ne suke taka rawar gani.

Mancine mai shekaru 49 ya ce "Ina murna da City take cikin daya daga kungiyar da ta yi fice a Ingila, kuma ni ne na hada 'yan wasan."

"Yan wasan da suke zurawa kungiyar kwallaye ni ne na kawo su da suka hada da Sergio Aguero da Edin Dzeko da Yaya Toure da David Silva da Samir Nasri", in ji Mancini.

Bayan da Mancini ya bar kungiyar, City ta dauki karin 'yan wasa Fernandinho da Alvaro Negredo wadanda suka zura kwallaye 23 tsakaninsu a kakar wasansu na farko da kungiyar.

Pellegrini yana harin daukar kofuna hudu da suka hada da Premier League da Champions League da FA Cup da kuma Capital One Cup.