Real Madrid ce ta fi arziki a duniya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tawagar 'yan kwallon Real Madrid

A karo na tara a jere, Real Madrid ce kungiyar kwallon kafa a duniya da ta fi kowacce arziki.

Sai dai kuma abin mamaki shi ne , Manchester United ta fado daga cikin jerin manyan kungiyoyi uku na farko ta fannin arziki a duniya.

Kamfani mai hada-hada a kan kasuwanci da cinikayya da kudade Deloitte ne ya fitar da alkaluman bisa lura da harajin da kungiyoyin su ka samu a kakar wasa ta shekarar 2012 zuwa 2013.

Jadawalin da kamfanin Deloitte ya fitar:

1. Real Madrid: Euro miliyan 518.9 2. Barcelona: Euro miliyan 482.6 3. Bayern Munich:Euro miliyan 431.2 4. Man Utd:Euro miliyan 423.8 5. Paris Saint Germain: Euro miliyan 398.8 6. Manchester City: Euro miliyan 316.2 7. Chelsea:Euro miliyan 303.4 8. Arsenal:Euro miliyan 284.3 9. Juventus: Euro miliyan 272.4 10. AC Milan:Euro miliyan 263.5

Karin bayani