Sunderland ta fitar da Man United

Image caption Sunderland za ta kara da Manchester City a wasan karshe na Capital One a filin Wembley.

Tabarbarewar Manchester United na dada tabbata bayan da Sunderland ta fitar da ita da fenariti daga gasar Capital One tare da hana ta buga wasan karshe da Manchester City a filin Wembley.

Bai fi minti biyu a kammala karin lokacin wasa ba, Phil Bardsley ya gigita golan United, David De Gea, inda ya zura masa kwallo a raga.

Sai dai saura 'yan sakankuna a busa usur Javier Hernandez ya farke, abinda ya jawo tafiya bugun fenariti.

Daga cikin kwallaye 10 da aka buga uku ne kawai suka shiga raga, inda aka tashi wasa Sunderland na da nasarar 2-1 kan Manchester United.

Hakan na nufin matukar ba abin da ba'a taba zata ba ne zai faru, wato Man U ta lashe gasar Zakar Turai a bana, Moyes zai kammala shekararsa ta farko a matsayin koci ba tare da kofi ko daya ba.