Masoyin Man United na kewar Sir Alex

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bara Ferguson ya bar kocin Man U bayan shekaru 26

Wani bugaggen magoyin bayan Manchester United ya kira lambar agajin gaggawa ta 999 ya na neman 'yan sanda su hada shi da Sir Alex Ferguson bayan da kungiyar ta sha kaye.

Mutumin da ke kauyen Crumpsall ya kira rundunar 'yan sandan Manchester ne da misalin 10:30 na dare bayan da Sunderland ta doke kungiyar a gasar kofin Capital One.

Rundunar ta ce rashin nasara a kwallo "abin takaici ne da bakin ciki" amma ya kamata jama'a su tuna cewa an ware lambar 999 ne domin neman agajin gaggawa.

Rundunar ta kuma shawarci mutumin da ya tuntubi kungiyar domin samun yadda zai iya magana da tsohon kocin.