Rosell ya yi murabus daga shubancin Barca

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sandro Rosell da Neymar

Shugaban kungiyar Barcelona, Sandro Rosell ya yi murabus bayan da wata kotun Spain ta yanke shawarar duba cinikin dan wasan Brazil Neymar da aka yi a bara.

Za a bincike Barca a kan zargin barnata kusan Euro miliyan 57 a yarjejeniyarsa da Santos.

Rosell a wani taron manema labarai ya bayyana murabus din inda mataimakinsa Josep Maria Bartomeu ya maye gurbinsa.

Rosell ya zama shugaban Barca ne bayan da ya kada Joan Laporta a zaben da suka yi a shekara ta 2010.