Micheal Essien ya koma AC Milan

Image caption Micheal Essien na Black Stars

Dan Ghana dake taka leda a Chelsea, Micheal Essien na gab da koma wa AC Milan.

Kocin Milan, Clarence Seedorf ya ce " Ana saran Micheal Essien zai zo nan bada jimawa ba".

Sai dai ba a sani ba ko Milan za ta karbin aron Essien ne ko kuma yarjejeniya ce ta dundundun.

Essien mai shekaru 31, ya koma Chelsea da Lyon a shekara ta 2005 kuma a kakar wasan da ta wuce ya tafi aro a Real Madrid.