Ba adalci a cinikin Mata - Wenger

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Wenger na jin Mata zai iya hana Arsenal cin kofin Premier

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce komawar Juan Mata daga Chelsea zuwa Manchester United ta bayyana rashin adalcin da ke cikin kasuwar 'yan wasa da ke ci a watan Janairu.

Tazarar maki biyu ne tsakanin Chelsea da Arsenal mai jagorar teburin Premier kuma ta kara da United sau biyu a kakar bana.

Hakan na nufin Mata ba zai yi wa Chelsea illa ba amma zai kara da Arsenal da Manchester City a gaba, abin da zai iya bai wa United wata dama a kansu.

"Akwai bukatar sauya lokacin da ake bude kasuwar sayen 'yan wasa domin tabbatar da adalci", in ji Wenger.