Zaha, Fabio da Jones za su koma Cardiff

cardiff Transfer Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cardiff City tana matsayi na karshe a teburin Premier

Cardiff na daf da daukar 'yan kwallon Manchester United Wilfried Zaha da Fabio Da Silva da dan wasan Stoke City Kenwyne Jones.

Zaha, mai shekaru 21 zai je kungiyar aro ne zuwa karshen kakar bana, Jones, mai shekaru 29 zai koma a matsayin musaya inda United za ta karbi mai zura kwallo a raga Peter Odemwingie.

Fabio, mai shekaru 23 zai koma Cardiff dungurun gum da wasansa, tuni likitocin kungiyar suka duba lafiyar 'yan wasan ranar Lahadi.

Tuni sabon kocin Cardiff Ole Gunnar Solskjaer ya dauki 'yan wasa uku zuwa kungiyar.

Zaha ya koma United ne dai daga Crystal Palace kan kudi £15 Miliyan a Janairun 2013, amma ya zauna a filin Selhurst Park aro har karshen kakar wasa.