FA: Man City za ta kara da Chelsea

pellegrini Mourinho
Image caption City za ta karbi bakuncin Chelsea a kofin FA

Manchester City za ta kara da Chelsea, ita kuwa Arsenal tana gida za ta karbi bakuncin Liverppol a kofin FA wasannin zagaye na biyar da aka raba jaddawali ranar Lahadi.

Kocin Everton Roberto Martinez zai fafata da tsohuwar kungiyarsa Swansea, Sunderland za ta barje gumi da Southampton a karawar haduwar kungiyoyin Premier.

Cardiff wadda take matsayi na karshe a teburin Premier tana gida domin karawa da mai rike da kofin FA Wigan, Hull kuwa za ta bakuncin Brighton da kuma wasan Sheffield Wednesday da Chalton a wasan kungiyoyin Championship.

Za a buga wasannin ne a karshen makon 15-16 Fabrairun bana.

Ga cikakken jaddawalin kofin FA

Manchester City v Chelsea

Sheffield United or Fulham v Nottingham Forest or Preston North End

Arsenal v Liverpool

Brighton & Hove Albion v Hull City

Cardiff City v Wigan Athletic

Sheffield Wednesday v Charlton Athletic

Sunderland v Southampton

Everton v Swansea City