United ta kammala cinikin Mata

Moyes Mata Hakkin mallakar hoto Man Unt
Image caption Dan kwallo na biyu da Koci Moyes ya kawo United

Juan Mata ya kammala komawa Manchester United daga Chelsea kan kudi £37.1 miliyan, kuma dan wasan da Kungiyar ta saya mafi daraja a tarihi.

Dan kasar Spain mai wasan tsakiya, tun a ranar Asabar Likitoci su ka duba lafiyarsa, ana tsammanin ya rattaba kwangila da kungiyar har zuwa shekara ta 2018.

Mata, mai shekaru 25 kila ya fara bugawa United wasan da za ta kara da Cardiff ranar Talata a kofin Premier.

Dan wasan ya zama na biyu da Koci David Moyes ya dauka tun komawarsa United, bayan da ya dauki dan kwallon Everton Marouane Fellaini a watan Disamba kan kudi £27.5 miliyan.

Mata, ya buga wa Spain wasanni 32, kuma United za ta gabatar da shi ga magoya bayanta ranar Litinin.