Milan ta kammala cinikin Essien

Micheal Essien Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Essien zai ci gaba da wasa a AC Milan ta Italiya

AC Milan ta kammala cinikin Micheal Essien tsohon dan kwallon Chelsea, bayan da ya rattaba hannu kwangilar watanni 17 da kungiyar.

Dan wasan mai shekaru 31 mai wasan tsakiya da ya fara buga gasar Premier a shekarar 2005, ana saran Milan za ta kaddamar da shi a gaban magoya bayanta ranar Talata a San Siro.

Kungiyoyin biyu dai sun amince da cinikin dan wasan ne a ranar Juma'a.

Dan wasan zai ci gaba da bugawa Milan wasanni har zuwa Yunin shekarar 2015.

Essien wanda Chelsea ta dauka daga Lyon kan kudi £24.4 Miliyan a dan wasanta da yafi daraja, ya buga wasanni tara kacal tun lokacin da ya dawo daga Real Madrid daga aro.