Wenger zai tsawaita kwantiraginsa da Arsenal

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wenger ya share shekaru 18 ya horas da Gunners

Kocin Arsenal Arsene Wenger zai tsawaita kwantiraginsa da Gunners, in ji shugaban gudanarwa na kungiyar, Ivan Gazidis.

Kocin da ya fi dadewa a gasar Premier yana karshen kwantaraginsa da kungiyar, wacce za ta kare a karshen kakar bana da kulob din na arewacin Landan.

Gazidis ya ce "Arsene zai tsawaita kwantiraginsa da mu, kuma za mu sanar a lokacin da ya kamata."

Wenger, mai shekaru 64, ya fara horaswa a Emirates tun a shekarar 1996.

Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da Gunners ta bayyana hada hulda ta miliyoyin fam da kamfanin yin kayayyakin wasanni na Jamus, wato Puma.

Gunners tana matsayi na daya a teburin Premier a bana da tazarar maki daya kacal tsakaninta da ta biyu, da tazarar rarar kwallaye 24 bayan da ta lashe wasanni bakwai daga cikin wasanni goma da ta buga a baya.

A shekaru 18 da Wenger ya yi a Arsenal ya lashe kofin Premier uku da kofin FA hudu da Community Shield hudu; rabon kungiyar da ta dauki gagarumin kofi tun a shekarar 2005.