'Ba zamu sayar da Messi ba'

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barcelona na burin dan wasan ya ci gaba da wasa a kungiyar

Shugaban riko na kungiyar Barcelona, Josep Maria Bartomeu, ya ce Lionel Messi ba na sayarwa bane, har ma kungiyar ta fara shirin tattaunawa domin tsawaita kwantiraginsa.

Ana ta rade-radin cewa Messi, mai shekaru 26 wanda ya lashe kyautar dan kwallo duniya sau hudu, kungiyar Paris St-Germain ta Faransa na zawarcinsa.

A wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan radiyon RAC1, wadda kuma Barca ta saka a shafinta na inatnet, Bartomeu ya ce: "Kungiyar za ta zauna da nufin tsara yadda za a tsawaita kwantiragin dan wasan."

Messi ya zura kwallaye 60 a wasanni 50 da ya buga a bara, sai dai ya samu tsaiko daga karshe lokacin da ya yi fama da jinya.

Yanzu ya zura kwallaye 18, takwas daga cikinsu a kofin La - liga, tun lokacin da ya zura kwallon karshe a Satumbar bara a lokacin da ya ji rauni ya kuma yi jinyar watanni biyar.