Baines ya sabunta kwangilarsa da Everton

Leighton Baines Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Dan wasan zai ci gaba da buga kwallo a Everton

Leighton Baines ya tsawaita kwangilarsa da Everton na karin tsawon shekaru hudu.

Tsohon kocin kungiyar David Moyes, sau biyu ya yi kokarin daukar dan wasan mai shekaru 29 dan kwallon Ingila zuwa Manchester United a bana.

Tun lokacin da Leighton Baines ya koma Everton ya bada kwallon da aka zura a raga har karo na 33 a kofin Premier, ya yiwa 'yan wasan baya masu taimakawa a zura kwallo da tazarar 14.

Everton ta dauko Baines daga Wigan kan kudi £6 Miliyan a shekarar 2007, kuma saura watanni 18 kwangilarsa ta kare da kungiyar.