Rabuwa da Mata ba dadi - Mourinho

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jose Mourinho da Juan Mata

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce da kyar ya amince wa dan wasan Spain Juan Mata ya koma kungiyar Manchester United.

Mata, mai shekaru 25 ne dan wasa mafi tsada da United ta saya a bana, inda ta saye shi kan £37.1miliyan daga Chelsea.

Mourinho ya shaida wa BBC cewa zai so a ce su na tare da Mata amma in ya rike shi bai yi masa adalci ba.

"Ina son mutane su kasance cikin farin ciki. Abin takaicin shi ne ba zai iya faranta masa ba a wannan kungiyar - na riga na sa Oscar a lamba 10."

Sai dai Mourinho ya ce duk ranar da Mata ya je filin Stamford Bridge tare da United, magoya bayan Chelsea za su yi masa kyakkyawar maraba.