Newcastle za ta sayi Luuk de Jong

Luuk de Jong Hakkin mallakar hoto AP
Image caption De Jong dan wasan Holand mai zura kwallo a raga

Dan kwallon Borussia Monchengladbach Luuk de Jong zai yi tattaki zuwa kungiyar Newcastle domin duba lafiyarsa da nufin bugawa kungiyar wasanni a matsayin aro.

Dan wasan Holland mai zura kwallo a raga, ya koma Jamus da kwallo kan kudi fan £12.6 Miliyan shekaru biyu da suka wuce, ya kuma zura kwallaye 45 a wasannin 86 lokacin da yake wasa a FC Twenty.

De Jong, mai shekaru 23 ya zura kwallaye 6 a gasar Bundesliga a kakar wasa ta bana.

Ana saran dan kwallon zai iya bugawa Newcastle wasa a ranar Asabar a karawar hamayyar tsakanin da Sunderland idan yarjejeniyar ta kullu.