Sunderland na daf da sayen Scocco

Ignacio Scocco Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan wasa na uku dan Argentina da yake Sunderland

Sunderland na daf da sayen dan kwallon Argentina mai zura kwallo a raga Ignacio Scocco, in ji kocin kungiyar Gus Poyet.

Scocco wanda yake buga kwallo da Internacional ta Brazil, likitocin Sunderland za su duba lafiyarsa da zarar an kammala cinikin dan kwallon.

Dan wasan mai shekaru 28, zai zamo dan kwallon Argentina na uku da kungiyar za ta dauka a watannan, tuni ta dauki Oscar Ustari da Santiago Vergini.

Sunderland tana matsayi na 19 a teburin Premier, ta kuma dauki mai tsaron bayan Fiorentina Marcos Alonso a matsayin aro, ta kuma maido da dan wasanta Conor Wickham da yake buga kwallo a Sheffield Wednesday.