Fulham za ta sayi Mitroglou

Konstantinos Mitroglou Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fulham tana matsayi na 19 a teburin Premier

Fulham na tattaunawa da kungiyar Olympiakos domin sayen dan wasanta mai zura kwallo a raga, Konstantinos Mitroglou.

Dan kwallon mai shekaru 25, dan wasan Girka ne zai kai kimanin kudi £11 miliyan, kuma Fulham tana kokarin kammala cinikin dan wasan kafin ranar Juma'a da za a rufe kasuwar musayar 'yan kwallon Turai.

Mitroglou mai tsawon kafa shida yana kan ganiyar wasansa a bana, ya zura kwallaye 21 a wasanni 23 da ya bugawa kungiyarsa da kasarsa, har da kwallaye uku da ya zura a raga.

Kwallaye ukun da ya zura su ne suka shigar da kasarsa zuwa gasar cin kofin duniya a wasan cike gurbi da suka doke Romania.