City ta bugi kirji duk da rashin riba

Kompany Zabaleta
Image caption shekaru biyu Manchester City na kirga rashin riba

Manchester City ta sanar da rashin riba a shekaru biyu a jere, inda ta bayyana faduwar £51.6 miliyan daga £97.9 miliyan a bara.

Rahotan da City ta fitar na kakar wasa 2012-13, ya fayyace cewa kungiyar wacce ita ce ta lashe kofin Premier a 2012, ta samu kudin shiga £271 miliyan.

Shugaban kungiyar Khaldoon Al Mubarak ya ce kungiyar tana samun gagarumin ci gaba a wasanninta, hakan ya samar da kafar tallata hajja ga kamfanoni.

Kungiyar tana matsayi na biyu a teburin Premier da tazarar maki biyu tsakaninta da Arsenal, za kuma ta iya darewa matsayi na daya idan ta doke Tottenham ranar Laraba.

Kocin kungiyar Manuel Pellegrini, ya kai City matakin siri biyu kwale a kofin zakarun Turai kuma karo na farko, sannan zasu buga wasan karshe a League Cup, kuma kungiyar ta kai wasan zagaye na biyar a kofin FA