An kusa a damfari Tottenham

Tottenham logo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tottenham ta gano kokarin da aka yi a damfareta

An kusa a damfari Tottenham bayan da wani dan Croatia ya yi kokarin sayar mata da dan wasa mai zura kwallo a raga dan kwallon Holland da sa hannun bogi.

Dan damfarar ya tuntubi Spurs a inda ya shaida musu cewar FC Twente ta umarce shi da ya sayar mata da dan wasan Holland mai shekaru kasa da 21 Luc Castaignos.

Kuma mutumin ya mikawa kungiyar takardun bogi da sa hannun shugaban Twente, sai dai Tottenham ta bincika ta kuma gane damfara ake son ayi mata.

Tuni aka sanar da hukumar kwallon Holland KNVB akan lamarin, ana fatan zata sanar da hukumar kwallon Turai Uefa da Fifa.