Seydou Keita ya koma Valencia

Seydou Kaita
Image caption Tsohon dan wasan Barcelon ya kuma koma Valencia

Dan kwallon Mali, Seydou Keita ya koma wasa a Valencia har zuwa karshen kakar wasan bana, a sanarwa da kungiyar ta bayar a ranar Alhamis.

Dan wasan mai shekaru 34, tsohon dan kwallon Barcelona ya koma kungiyar bayan da yarjejeniyarsa ta kare da kungiyar Dalian Aerbin ta China.

Valencia ta sanar a shafinta na Internet cewar Keita zai buga mata kwallo har zuwa 30 ga watan Yuni da kuma yarjejeniyar tsawaita kwangilarsa shekara daya.

Keita ya lashe kofuna 14 a shekaru hudu da ya bugawa Barcelona wasanni daga shekarar 2008 zuwa 2012, ya kuma bugawa Mali wasanni 88 ya kuma zura kwallaye 24 a raga.