Ramsey zai yi jinyar makwanni shida

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ramsey da Ozil na taimakawa Arsenal sosai.

Dan kwallon Arsenal Aaron Ramsey zai yi jinyar makwanni shida, kamar yadda kocinsa Arsene Wenger.

Dan shekaru 23, Ramsey ya ji rauni ne a wasansu da West Ham a watan Disambar bara.

Kenan jinyar za ta sa ba zai buga wasu muhimman wasanni ba wato karawarsu da Liverpool da Manchester United, da kuma wasan zakarun Turai tare da Bayern Munich.

Tun a shekara ta 2015 rabon da Arsenal ta lashe wata gasa.

Karin bayani