'Yan wasa sun yi wa Santander tawaye

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan wasan sun shiga fili amma sun ki taka leda.

'Yan kwallon kungiyar Racing Santander da ke buga wasa a La Liga sun ki taka leda a wasan daf da na kusa da na karshe na gasar Copa del Rey tsakaninsu da Real Sociedad saboda rashin biyan su albashinsu.

Hakan na nufin Sociedad ta yi nasara a wasan kuma za ta buga da Barcelona a matakin kusa da na karshe.

A ranar Litinin ne dai 'yan wasan Santander su ka sanar da kauracewa wasan, matukar shugaban kungiyar Angel Lavin da daraktocinsa ba su sauka daga mukaminsa.

'Yan wasan sun ce an kwashe watanni da dama ba a biya su kudinsu ba.