Kurt Zouma ya koma Chelsea

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kurt Zouma zai ci gaba da zama a St Etiene

Chelsea ta kamalla sayen dan kwallon St Etienne Kurt Zouma mai shekaru 19 a kan fan miliyan 12.

Dan wasan Faransa, mai shekaru 21 ya koma Chelsea a kan yarjejeniyar shekaru biyar da rabi amma zai ci gaba taka leda a St Etiene har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Haifaffen Lyon, Zouma ya hade da St Etienne tun yana da shekaru 15 a shekara ta 2009.

Ya buga wa kungiyar wasanni 52 inda ya zura kwallaye hudu.

Karin bayani