"City ba ta taka rawar da ta dace ba"

Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mourinho yace City bata cimma nasarorin da ake tsammata

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce Manchester City ba ta cimma nasarorin da aka tsammanta mata ba tun lokacin da Sheikh Mansour ya sayi kungiyar a shekarar 2008.

City ta lashe kofin FA a shekarar 2011 da kofin Premier a 2012, amma karo daya kacal ta haura wasan rukuni a kofin zakarun Turai a shekaru uku da ta fafata a gasar.

Mourinho ya fada kafin su kara ranar Litinin cewa "Sun lashe kofin Premier daya da 'yan kofuna kuma."

"Kungiyar tana da kyau matuka kuma sun hada hazikan 'yan wasa, amma ba sa lashe kofuna."

Mansour, ya kashe sama da £700 miliyan wajen sayen 'yan wasa tun lokacin da ya sayi City, ya kuma amince aka kawo fitattun 'yan kwallo da suka hada da David Silva da Yaya Toure kungiyar.

Ba su haura wasan rukuni ba a kofin zakaru na shekarar 2011-12 da 2012-13, za su karbi bakuncin Barcelona a bana ranar 18 ga watan Fabrairu.

A shekaru uku a kofin zakarun Turai tun shekarar 2008, ba su taba kai wasan daf da na kusa da karshe ba.

Ranar Litinin City za ta karbi bakuncin Chelsea a kofin Premier wasan mako na 24, City dai tana matsayi na biyu da maki 53 sai Chelsea da maki 50 a matsayi na uku.