Ruwan sama ya hana wasan Roma da Parma

Franco Totti Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yadda ruwa ya kwanta a filin wasa kenan

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya barke yasa an dage karawa tsakanin Roma da Parma, bayan minti takwas da fara wasa a kofin Serie A na Italiya.

Saukar ruwan yasa filin Stadio Olimpico ya taru da ruwa makil da yake hana tafiyar kwallo akan ciyawa.

Nan take alkalin wasa Andrea De Marco ya tsaida wasa ya kuma sanar da 'yan kwallon cewa kwallo bata tafiya kamar yadda ya kamata, saboda haka ya yanke hukuncin dage wasan.

Karawar dai itace ta mako na 22, kuma Roma tana da maki 50 a matsayi na biyu a teburi, Parma na matsayi na takwas da maki 32.