Kila Villa ba zai buga karawa da Madrid ba

David Villa
Image caption Dan wasan sai sauya shi aka yi a wasa da Real Sociedad

Kila dan kwallon Atletico Madrid mai zura kwallo a raga David Villa ba zai buga kofin Copa del Rey ba, a wasan daf da na karshe da za su kara da Real Madrid ranar Laraba.

Mai shekaru 32 ya ji rauni a cinyarsa a lokacin da suka kara da Real Sociedad suka kuma lashe wasan da ci 4-0, sai dai an sauya dan wasan a minti na 41.

Sai dai dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo zai buga a karawar da za suyi a Bernabeu duk da jan katin da aka ba shi a wasan da suka buga da Athletic Bilbao a ranar Lahadi.

Dan kwallo mafi tsada da Real ta saya Gareth Bale kan kudi £85 miliyon, wanda bai samu damar karawar da suka ta shi wasa 1-1 ba ranar Lahadi ana sa ran zai buga wasan.

Bale mai shekaru 24 ya buga wasanni 13, duk da raunin da yake fama a cinyarsa da kafa, duk da haka ya zura kwallaye 10 a raga.

Dukkan kungiyoyin biyu sun sami nasarar lashe kofin Copa del Rey, a inda Atletico ta dauki kofin karo 10, Real kuma ta dauka karo 18.