Laudrup zai ci gaba da kasancewa kocin Swansea

Michael Laudrup Hakkin mallakar hoto huw evans picture agency
Image caption Kocin yana fama da koma baya a kakar wasan bana

Shugaban kungiyar Swansea Huw Jenkins ya karyata rade-radin cewar kungiyar ta zauna domin fayyace makomar koci Michael Laudrup a kungiyar.

An dade ana rade- radin makomar Laudrup tun lokacin da kungiyar ta sha kashi a hannun West Ham ranar Asabar da ci 2-0.

Kuma karo na shida ana doke su a kofin Premier, sauran maki biyu su koma matsayin kungiyoyin da za su iya fadowa daga gasar Premier a bana.

Jenkins yace "Bani da masaniya akan taron makomar kocin mu, bamu taba maganarsa ba ko shirin tattaunawa akan makomarsa da mu ba."

Swansea ta fado matsayi na 12 a teburin Premier, sai dai ta baiwa abokiyar hamayyarta Cardiff tazarar maki uku wacce take matsayi na biyun karshe a teburi.