'Chelsea ba ta takarar lashe gasar premier'

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Mourinho ya ce Arsenal da City ne ke takara

Kocin Chelsea, Jose Mourinho ya ce kungiyarsa ba ta cikin masu kokawar lashe gasar premier ta bana duk da nasararsa da ta yi a kan Manchester City a filin Etihad.

Branislav Ivanovic ne yaci kwallon inda a yanzu City da Chelsea ke kankankan a yawan maki, a yayinda Arsenal ta basu tazarar maki biyu a saman teburin gasar.

Mourinho ya ce " takarar tsakanin manyan kungiyoyi ne biyu, watakila a kakar wasa mai zuwa ne zamu shiga ciki".

Nasarar da Chelsea ta yi a filin Etihad ya nuna cewar, kungiyar ta zama ta farko da ta doke Manchester City gida-da-waje a gasar Premier tun abinda Everton ta yi a kakar wasa ta 2010-11.

Chelsea ta cancanci samun nasara musamman yadda 'yan wasanta suka shafa na City.

Karin bayani