Najeriya da Ivory Coast za su kara a Amurka

Drogba Mikel Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasannin sada zumunci domin tunkarar Brazil a bana

Najeriya da Ivory Coast za su kara a wasannin sada zumunci a Amurka domin shirye-shiryen gasar kofin duniya da zai kunshi har da zakarar kofin duniya Spain.

Hukumar kwallon Amurka MLS ce ta shirya wasannin da ta bashi sunan "Wasanni domin tunkarar Brazil" da zai kunshi kasashe daga kudancin Amurka da za a fara ranar 27 ga watan Mayu zuwa 10 ga watan Yuni.

Girka da Ivory Coast da Honduras da Bosnia da Herzegovina su ne sauran kasashen da za su buga kofin duniya suka kuma amince su shiga wasan.

Bolivia da El Salvador wadanda ba su sami gurbin shiga kofin duniya da Brazil za ta karbi bakunci a bana ba, suma suna daga cikin wadanda za a fafata da su.

MLS tace za ta sanar da jaddawalin wasannin da kuma filayen da za a fafata a wasannin.