'Ban damu da ban koma Stoke ba'

Jonathan Pitroipa
Image caption Pitroipa yace yana fatan ya buga wasa a Premier

Jonathan Pitroipa dan kwallon Burkina Faso ya ce bai damu ba, da bai koma kungiyar Stoke City ba daga Rennes a ranar karshen rufe kasuwa musayar 'yan kwallo.

Stoke da Rennes sun amince da yarjejeniyar daukar dan wasan a aro, idan kuma ya taka wasa mai kyau ta saye shi.

Pitroipa ya shaidawa BBC cewa "Daf ya rage na koma Stoke City, amma kila lokaci ne bai yiba"

"Premier gasa ce da ya dace na taka wasa ko da anan gaba ne, amma a yanzu na cire abinda ya faru a satin da ya gabata", in ji Pitriopa.

An zargi mai kula da wasan Pitroipa da jami'an da suka shiga tsakanin kungiyoyin biyu da kawo tsaiko a lokacin cinikin dan wasan.

Sai dai dan wasan mai shekaru 27 da ya bugawa Rennes wasanni 23 a kakar wasan bana, ya kara da cewa an samu matsala a ranar karshe ne, amma babu hannun mai kula da wasana a tsaikon koma wata Stoke.