Swansea za ta sauya mataimakan koci

Michael Laudrup Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin na fama da koma baya a kungiyar a bana

Tsohon kaftin din Swansea na daf da karbar matsayin mataimakin kocin Swansea, Gary Monk a kokarin da kungiyar take na sauye-sauyen masu taimakawa Micheal Laudrup.

Sai a ranar Talata Laudrup ya koma kungiyar bayan tafiyar da yayi Paris na kwana biyu tun lokacin da West Ham ta doke su da ci 2-0.

Swansea tana matsayi na 12 a teburin Premier, maki biyu tsakaninta da Cardiff abokiyar hamayya da za ta karbi bakunci ranar Asabar.

Wannan sauyin ya kawo shakku game da makomar masu taimakawa koci da suka hada da Larsen da Morten Wieghorst da Oscar Garcia.

Daukan wannan mataki a locin da Laudrup yayi tafiya, zai iya kawo kace nace akan makomar kocin.