Fulham ta daki Burji - Meulensteen

Rene Meulensteen
Image caption Kocin ya bukaci 'yan wasa su saka kaimi a wasanninsu

Kocin Fulham Rene Meulensteen ya yi kira ga 'yan wasa cewa su tashi tsaye su fitar da kungiyar daga halin da take ciki tunda sun tunkuyi burji.

Fulham tana matsayi na karshe a teburin Premier kuma Sheffield United ta fidda ita a kofin FA ranar Talata.

Koci Fulham Meulensteen ya ce "Mun sani babu wanda zamu zarga in banda kanmu, ya kamata kowa ya duba tsabar idon dan uwansa domin neman mafuta."

Bayanda suka tashi wasan farko 1-1 da Sheffield United, a wasa na biyu aka doke Fulham har gida da Shaun Miller ya zura kwallo a karin lokaci.