An dakatar da Ronaldo wasanni uku

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan wasan zai huta har wasanni uku a kofin La-liga

An dakatar da Cristiano Ronaldo buga wasanni uku, bayan da aka bashi jan kati a karawar da suka yi da Athletic Bilbao ranar Lahadi.

Sai dai an amince dan kwallon ya buga wasan Copa del Rey a zagayen gab dana karshe da zasu kara da Atletico Madrid ranar Laraba.

Ana saran Gareth Bale wanda bai buga karawa da Bilbao ba, zai buga wannan wasan a filin Bernabeu.

Ronaldo ya karbi jan kati kai tsaye bayan da suka yi karo da dan kwallon Athletic Carlos Gurpegi, ya kuma karbi karin guda biyu bayan da ya gyda kansa lokacin da zai bar fili.

Dan wasan ba zai buga karawar da Madrid zata yi da Villarreal da Getafe da Elche, sai dai idan kungiyar ta daukaka kara kuma FA ta saurare ta.