"Kinnear ya yi aiki na gari a Newcastle"

Joe Kinner Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Watanni bakwai ya yi a matsayin daraktan wasanni

Kocin Newcastle Alan Pardew ya ce Daraktan wasannin kungiyar da ya ajiye aik Joe Kinneri, ya yi kokari da yadda ya gudanar da aikinsa, kuma ya ji takaicin barinsa kungiyar.

Mai shekaru 67, wanda ya sanar da ajiye aikinsa ranar Litinin, ya kasa sayo dan wasan da zai zauna a kungiyar dindin din a tsawon watanni bakwai da ya yi yana aiki.

Pardew yace "nakanyi bakin ciki idan naga wani ya rasa aikinsa, kamar yadda naga Joe yayi."

Newcastle ta sayar da mai wasan tsakiya Yohan Cabaye da ake hanken shi ne dan kwallon kungiyar da yafi fice zuwa PSG kan kudi £19 miliyan a Janairu lokacin musayar 'yan kwallo.

Koda yake kungiyar ta kasa maye gurbin dan kwallon data sayar, duk da taya dan wasan Lyon Clement Grenier da aka ki sayar mata da shi.

'Yan kwallo biyu kacal Kinner ya kawo kungiyar da suka hada da Luuk de Jong daga Borussia Monchengladbach da Loic Remy daga , QPR a aro a matsayinsa na daraktan wasanni.