Zan koma haskakawa - Messi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Lionel Messi da Neymar sune manyan 'yan wasan Barcelona

Dan kwallon Barcelona da Argentina, Lionel Messi ya ce yanada kwarin gwiwa zai koma haskaka tun kafin a soma gasar cin kofin duniya a bana.

Dan shekaru 26, sau biyu yana jinyar rauni a kakar wasan bana.

Yace "Ina da kwarin gwiwa kuma inda saran koma matakin da na saba a fagen tamaular duniya".

Messi ya yi jinyar makwanni uku saboda rauni a cinyarsa a farkon kakar wasa ta bana, sannan kuma ya kara shafe watanni biyu saboda ciwon kafa.

Barcelona ce ta biyu a kan teburin La Liga inda Atletico Madrid ke kan gaba.

Karin bayani