Za a fara wasannin Olympics a yau

Wurin da za a gudanar da wasannin Olympics a wurin shakatawa a Sochi. Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An girke sojoji da 'yan sanda masu tarin yawa dan tabbatar da tsaro a wurin da za a gudanar da wasannin hunturu na Olympics.

Nan gaba a yau ne za a bude fara gasar wasan Olympics ta hunturu a garin Sochi na kasar Rasha inda aka tsaurara matakan tsaro.

Mataimakin Prime Ministan Rasha Arkady Dvorkovich ya shaidawa BBC cewa an girke fiye da sojoji dubu arba'in da kuma 'yan sanda masu dumbin yawa a wajen da za a gudanar da wasan.

Ana saran shugabannin kasashen duniya da yawa za su halarci wurin, sai dai wasu shugabannin sun kauracewa wajen, don nuna adawarsu da wata doka da Rasha ta yi ta hana abinda ta kira farfagandar 'yan luwadi da madigo.

Shugaba Obama ma ba zai halarci wurin ba yana cewa Rasha na da gagarumin aiki na hana afkuwar harin ta'addanci a wurin.

Ya kuma kara da cewa Amurka za ta taimaka wajen tsare lafiyar 'yan wasa.

Karin bayani