Da kyar mu kare kambunmu - Rooney

Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dan wasan na fatan United ta kare a 'yan hudun farko

Dan kwallon Manchester United Wayne Rooney yace da kyar ne idan zasu iya kare kofin Premier a bana.

United mai rike da kofi zata kara da Fulham ranar Lahadi, tana matsayi na bakwai da tazarar maki 16 tsakaninta da Chelsea wacce take matsayi na daya a teburin Premier.

Rooney yace "hakika matsayi na hudun farko muke fatan karkarewa."

"Koda yaushe muna fatan lashe kofi, amma wannan karon ya mana nisa, kamar da wuya mu dauka a bana."

United tayi rashin nasarar wasanni takwas daga cikin 24 data kara a kofin Premier a bana tun lokacin da David Moyes ya karbi ragamar horas da United daga Sir Alex Ferguson.