City ta yi kama da motar Jaguar - Mourinho

Jose Mourinho
Image caption Har yanzu kocin bai ce kungiyarsa za ta lashe Premier ba

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya kamanta Manchester City da motar Jaguar, haka kuma ya ce kungiyar Manuel Pellegrini ce ake hasashen za ta lashe kofin Premier a bana.

Dan kwallon Chelsea Eden Hazard ne ya zura kwallaye uku rigis a ragar Newcastle lokacin da suka kara ranar Asabar suka kuma dare matsayi na daya a teburin Premier.

Mourinho ya fada ranar Litinin cewa kungiyarsa karamin doki ne a tseren lashe kofin Premier.

Kocin wanda ya kashe kusan £48 miliyan a sayen sabbin 'yan kwallo a Janairu, bai ce kungiyarsa za ta lashe kofin Premier ba wadda rabonta da shi tun shekarar 2009-10, duk da kungiyar ta buga wasanni 10 ba a doke ta ba a Premier.