Tottenham ta doke Everton daci 1-0

Tottenham Everton Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Adebayo sai haskakawa yake a kakar wasan bana

Kungiyar Tottenham ta doke Everton daci daya mai ban haushi a kofin Premier wasan mako na 25.

Emmanuel Adebayo ne ya zura kwallo a raga da ya baiwa Tottenham maki uku a kokarin da kungiyar take na neman gurbin buga gasar kofin zakarun Turai.

Dan wasan ya karbi kwallo cikin sauri a dukan Free-kick ya kuma buga ta wuce gola Tim Howard da hakan ya kai Spurs matsayi na biyar a teburin Premier.

Rashin nasara da Everton tayi yasa ta koma matsayi na shida a teburi da tazarar maki shida tsakaninta da Liverpool wacce take matsayi na hudu a teburin Premier.