Watakila a dakatar da Bellamy

Craig Bellamy Hakkin mallakar hoto huw evans picture agency
Image caption FA na jiran rahotan alkalin wasa kafin ta dauki mataki

Watakila a dakatar da dan kwallon Cardiff City, Craig Bellamy na tsawon wasanni uku, bayan da aka ga alamar ya tokari dan kwallon Swansea, Jonathan de Guzman a karawar da suka yi ranar Asabar.

Lamarin ya auku lokacin wasan da Swansea ta doke su da ci 3-0, amma hukumar kwallon kafa ta Ingila wato FA na jiran rahoton alkalin wasa Andre Marriner kafin ta yanke hukunci.

Bellamy mai shekaru 34 ya yi wa Guzman gula da gwiwar hannunsa bayan an dawo zagaye na biyu a filin wasa na Liberty.

Doke Cardiff City da aka yi ya kaita matsayi na 19 a teburin Premier kuma zata karbi bakuncin Aston Villa a gida ranar Talata.

Bayan karawa da Villa, Cardiff za kuma ta karbi bakuncin Wigan a kofin FA, sannan ta kara da Hull a kofin Premier.