Zamu kara kaimi a wasannin mu- Solskjaer

Ole Gunner Solskjaer Hakkin mallakar hoto huw evans picture agency
Image caption Kocin yace zasu saka kaimi domin ci gaba da zama a gasar Premier

Kocin Cardiff City Ole Gunner Solskjaer ya ce kungiyarsa za ta mance da doke ta 3-0 da Swansea, kuma za ta saka kaimi na ganin ta ci gaba da buga kofin Premier a bana.

Doke Cardiff da a kayi yasa ta koma matsayi na 19 a teburin Premier.

Za kuma ta kara da Aston Villa wacce take matsayi na 12 a teburi ranar Talata, Solskjaer yace wasa ne na karin batta.

Tsohon dan kwallon Manchester United mai zura kwallo ya lashe wasa daya aka kuma doke su wasanni hudu daga cikin wasanni biyar a kofin Premier tun lokacin da ya maye gurbin Malky Mackay.