Watakila a dakatar da Yaya Toure

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yaya Toure ne gwarzon dan kwallon Afrika na 2013

Watakila a dakatar da dan kwallon Manchester City, Yaya Toure na tsawon wasanni uku, bayan da aka ga alamar ya tokari dan kwallon Norwich, Ricky van Wolfswinkel.

Lamarin ya auku lokacin wasan da suka tashi babu ci tsakaninsu da Norwich, amma hukumar kwallon kafa ta Ingila wato FA na jiran rahoton alkalin wasa Jon Moss kafin ta yanke hukunci.

Ba za a ladabtar da Toure ba idan har alkalin wasa Moss ya ga lokacin da abin ya faru, amma idan har bai gani ba, hukumar FA za ta duba bidiyon wasan, don ta ladabtar da shi.

Idan har hukumar ta FA ta yanke cewar ya kamata a baiwa Toure katin gargadi ne, to za a rufe batun, amma idan har ya cancanci jan kati ne, to za a dakatar da shi na wasanni ukku.

Karin bayani