Mun kara samun koma baya — Moyes

David Moyes Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Mun taka wasa amma bamu da nasara a lokacin

Kocin Manchester United David Moyes ya ce zura musu kwallo da a kayi daf a tashi wasa, ya yi tsauri bayan da kungiyar ta kasa lashe wasa karo na 13 a wasannin 25 na kofin Premier a bana.

Liverpool wacce take matsayi na hudu a teburin Premier ta bai wa United tazarar maki tara a kokarin da take na neman gurbin zuwa gasar zakarun Turai.

Darren Bent ya zura kwallaye hudu a filin Old Trafford, shi ne dan kwallo da ya zarta duk wani dan wasa zurawa United kwallo a filinta.

United tana da maki 41 bayan buga wasanni 25 a kofin Premier bana.

Moyes yace "Haka muke ta fama a kakar wasan bana, ranar Lahadi tayi tsauri, mun taka kwallo amma muka tashi da maki daya."