Wasan Fulham da Liverpool ba tabbas

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Filin Craven Cottage na Fulham

Za a iya dage wasan Fulham da Liverpool na rukunin Premier ranar Laraba idan ma'aikanta jiragen kasa na birnin London su ka gudanar da yajin aikin da su ka shirya.

Ranar Talata ne ma'aikatan jiragen kasar za su shiga yajin aikin kwanaki biyu, abinda zai iya haddasa tarnaki ga zirga-zirga a London, irin wacce aka fuskanta makon jiya.

Fulham na fargabar cewa ma'aikatanta masu kula da filin wasa ba za su hallara akan lokaci ba idan yajin aikin ya tabbata.

Kan haka ne kungiyar ta ce za ta fitar da sanarwa ranar Talata da karfe 15:00 GMT game da ko wasan zai yiwu ko a'a.

Sai dai kungiyar Arsenal ta tabbatar da karonta da Manchester United ranar Larabar zai gudana ko da ma'aikatan jiragen kasan su na yajin aiki.

Karin bayani