Ferdinand bai shirya ritaya ba - Moyes

Rio Ferdinand Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan na fama da jinya a kakar wasan bana

Kocin Manchester United David Moyes ya karyata rahotan cewa Rio Ferdinand ba zai samu halarta zuwa Dubai da kungiyar za tayi, har ma wai dan wasan na shirin yin ritaya.

Mujallar The Sun ce ta wallafa cewar Ferdinand mai shekaru 35, baya cikin tawagar kungiyar da za tayi atisaye a Dubai.

Moyes yace " Abinda aka rubuta ba gaskiya bane, ba shi da tushe balle makama".

Manchester United wacce za ta kara da Arsenal ranar Laraba an bata tazarar maki 15 tsakaninta da Chelsea mai matsayi na daya, da kuma tazarar maki tara tsakaninta da Liverpool.