Wasan Arsenal da ManU ya ci 'yan kallo

Image caption Wasan da aka yi a Emirates bai yi armashi ba.

Arsenal ta kasa komawa saman teburin Premier bayan da ta yi canjaras da Manchester United a filin Emirates.

Gunners din dai na fatan murmurewa ne daga ragargazar 5-1 da Liverpool ta yi musu yayin da Jajayen Shaidanu ke son farfadowa daga kunnen dokin 2-2 da su ka yi a gida da Fulham da ke kasan tebur.

Hakan ya sa wasa bai armashi ba kuma bai biya bukatar kocin Arsenal Arsene Wenger ko na United David Moyes ba.

Sakamakon wannan wasan Arsenal na nan a mataki na biyu yayin da United ke mataki na bakwai.