An gayyaci Yobo cikin Super Eagles

Joseph Yobo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yobo yafi duk wani dan wasa yawan buga wa Najeriya wasanni

Najeriya ta gayyaci dan kwallon Norwich City Joseph Yobo domin buga ma ta wasan sada zumunci da za ta kara da Mexico ranar 5 ga Maris a Amurka.

Rabon dan wasan mai shekaru 33 da ya buga wa Najeriya wasa tun lokacin da kasar ta lashe kofin Afirka a bara a Afirka ta kudu.

Yobo wanda ya bugawa Najeriya wasanni 93, ya samu damar da zai iya buga mata kofin duniya.

Stephen Keshi ya ce "Na sha fada a koda yaushe cewar Yobo shi ne Kaftin, kuma zan kira shi tawagar 'yan wasa a duk lokacin da ya dace, kada mutane su yi mamaki.

Haka kuma kocin ya kira 'yan wasa uku sababbi da suka hada da Imoh Ezekiel da Ramon Azeez da Michael Uchebo da za su buga wasan sada zumuncin.