''Da kyar Cole zai samu gurbi a wasan Ingila''

Ashley Cole
Image caption Dan wasan yana fama da kalubale a kakar wasan bana

Kocin tawagar Ingila Roy Hodson ya ce zai yi wuya dan kwallon Chelsea Ashley Cole ya samu gurbi a cikin 'yan wasansa sha dayan farko a gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil.

Cole, mai shekaru 33, ba ya samun bugawa Chelsea wasa a kai a kai a kakar wasan bana, kuma yana fuskantar kalubale wajen dan kwallon Everton Leighton Baines a gurbin bugawa Ingila wasa.

Hodson ya ce, "Shekaru da dama ana kalubalantar dan wasan, yanzu ya rage gare shi ya sa kaimi."

Kocin ya bayyana cewar ba zai kira dan kwallon Chelsea John Terry zuwa tawagar 'yan wasan Ingila ba domin buga mata kofin duniya.

Terry, mai shekaru 33, ya yi ritaya daga bukawa Ingila kwallo a Satumbar 2012, amma ana ta kiraye kirayen a dawo da dan kwallon don ya bugawa Ingila wasa ganin yadda yake saka kaimi a kakar wasan bana.