Cardiff ta zargi Mackay da jawo asara

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Korarren kocin Cardiff, Malky Mackay.

Kungiyar Cardiff City ta soki tsarin cinikin 'yan wasa na tsohon kocinta Malky Mackay, inda ta ce ya jawo ma ta asarar miliyoyin famafamai.

Shugaban kungiyar Simon Lim ya ce sun yi asarar fiye da £8.5 miliyan a cinikin dan wasan gaba Andreas Cornelius.

Sai dai kungiyar kociyoyi ta Premier ta ce babu wani cinikin da tsohon kocin ya yi ba tare da amincewar shugaban kungiyar ba.

Cinikin Cornelius dai na cikin dalilan da su ka sa mai kungiyar Vincent Tan ya kori jami'an daukar 'yan wasa Ian Moody a Oktoba sannan ya cire Mackay daga koci bayan watanni biyu.